Chamakh ya bar Arsenal

marouane chamakh
Image caption Bayan Chamakh Crystal Palace ta dauki Kevin Phillips da Dwight Gayle

Marouane Chamakh ya bar Arsenal ya koma Crystal Palace na tsawon shekara daya.

Dan wasan na kasar Morocco mai shekara 29 zai sanya wa kungiyar riga mai lamba 29 ne bayan da aka tantance lafiyarsa.

Arsenal ta dauke shi ne a shekara ta 2010 daga Bordeaux ta Faransa.

Bayan kwallaye 11 da ya ci a Shekararsa ta farko a London, guda uku kawai ya ci a shekaru biyu da suka biyo baya.

Arsenal ta bayar da shi aro ga West Ham a watan Janairu amma kuma sau uku ya yi wasa.

Chamakh shi ne dan wasan gaba na uku da Crystal Palace ta saya a wannan lokacin.

Kungiyar za ta fara wasanta na bana da Tottenham ranar Lahadi.

Karin bayani