Stewart Downing zai koma West Ham

Image caption Stewart Downing

Kungiyar West Ham United ta amince tsakaninta da Liverpool a kan sayen Stewart Downing.

Dan Ingila mai shekaru 29, ana saran za a gwada lafiyarsa kafin ya koma Upton Park.

Downing ya kulla yarjejeniya da Liverpool a kan pan miliyon 20 daga Aston Villa a watan Yulin 2011.

Idan ya koma West Ham, Downing yabi sawun Andy Carroll wanda ya canza sheka daga Anfield zuwa Upton Park.

Carroll ya koma Liverpool daga Newcastle a kan pan miliyon 35 a watan Junairun 2011 amma ya koma West Ham a yarjejeniya kan pan miliyon 15.

Karin bayani