Malawi na son a sauya wasan Calabar

Image caption Kocin Malawi Tom Saintfiet

Hukumar kwallon kafa ta Malawi-FAM ta bukaci FIFA ta dauke wasan da za su buga da Najeriya daga Calabar zuwa wani birnin.

Hukumar ta FAM ta koka game da nada Hamada el Moussa Nampiandraza a matsayin alkalin wasan.

Kocin Malawi, Tom Saintifiet, ya ce sun bayyana bukatarsu ce saboda babu jirgin sama da ke zuwa kai tsaye birnin Calabar daga kasashen waje, yana mai cewa ya kamata a mayar da wasan zuwa Abuja ko Legas.

A cewarsa, ba za a samu kasaitaccen makwanci a Calabar ba saboda ba babban birni ba ne.

Najeriya na gaban Malawi da maki biyu, kuma duk kasar da ta samu nasara ita ce za ta tsallake zuwa zagaye na gaba, don buga Gasar cin Kofin Duniya.

Karin bayani