Mikel ba zai yi wa Najeriya wasa ba

mikel obi
Image caption Keshi ya shawarci Mikel Obi ya ci gaba da zama a Chelsea

John Mikel Obi ya janye daga tawagar Najeriya da za ta yi wasa da Afrika ta Kudu a gobe Laraba.

Obi ba zai yi wasan ba na sada zumunta a birnin Durban na Afrika ta Kudun saboda ciwon ciki.

Saboda hakan likitocin Chelsea suka rubuta wa hukumar kwallon kafa ta Najeriya kan ta fitar da shi daga tawagar.

Mai horad da 'yan wasan Najeriya Stephen Keshi ya amince inda ya ce ba zai so ya matsa wa dan wasan ba.

Saboda wasan da Najeriyar za ta yi da Malawi ranar 7 ga watan Satumba na neman zuwa gasar kofin Duniya a Calabar.

Dukkanin sauran 'yan wasan 19 na Najeriya sun hallara a Durban din ciki har da Victor Moses abokin wasan Obi a Chelsea.

Karin bayani