Carrick ya fice daga tawagar Ingila

Dan wasan tsakiya na Mancheter United da kuma Ingila, Michael Carrick
Image caption Wasan Ingila da Scotlan na zuwa ne kwana uku kafin fara kakar wasannin premier league

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon Ingila, Michael Carrick ya fice daga tawagar kungiyar, saboda ciwon ido.

Hakan na zuwa a daidai lokacin da kungiyar ta Ingila za ta yi wasan sa da zumunci da takwararta ta Scotland a ranar Laraba.

Dan wasan na kulob din Manchester United ya kasance na biyu, bayan Ashley Young wanda shi ma ya fice daga tawagar saboda raunin da ya samu.

A bangaren 'yan wasan Scotland kuwa, Liam Bridcutt ne kadai baya cikin tawagar 'yan wasanta 29.