Tennis: Andy Murray ya farfado

andy murray
Image caption Murray na neman yin nasara a wasanninsa kafin ya kare kambunsa na Gasar US Open da za a fara 26 ga Agusta

Andy Murray ya farfado daga kashin da ya sha a makon da ya gabata da aka fitar da shi a farko-farko a gasar tennis ta Montreal a Canada.

A wannan karon Murray dan Birtania yayi nasara akan Mikhail Youzhny na Rasha a zagaye na biyu na gasar Cincinnati.

Murray na biyu a duniya kwanaki biyar da suka gabata ya sha kashi a hannun Ernests Gulbis a Montreal amma a wannan karon cikin sauki ya fitar da Youzhny da maki 6-2 6-3.

Ranar Alhamis Murray zai kara da Julien Benneteau a zagayen 'yan 16.

Roger Federer da Rafeal Nadal na daga wadanda ake saran zasu yi wasan kusa da karshe da Murray, shi kuwa Novak Djokovic ka iya fuskantar wani daga cikinsu a wasan karshe.

Tommy Haas ya buge Marcel Granollers 6-4 6-1 zai hadu da Roger Federer yayin da Juan Martin del Potro ya yinasara akan Nikolay Davydenko 7-5 7-5.

A bangaren mata Serena Williams ta fitar da Eugenie Bouchard 'yar Canada 4-6 6-2 6-2

Karin bayani