Amurka za ta yi wa filin wasa rufi saboda ruwa

arthur ashe stadium
Image caption Bayan filin wasan na Arthur Ashe hukumar tennis ta Amurka zata samar da wasu sababbi biyu

Hukumomin gasar tennis ta Amurka US Open za su yi wa babban filin wasan gasar rufi saboda hana ruwan sama kawo cikas ga wasan.

Hukumomin sun bayyana shirin samar da rufin da za a rika janye shi idan ba a ruwa a filin wasa na Arthur Ashe da ke New York.

Shekaru biyar a jere da suka gabata an rika dage wasan karshe na maza na gasar saboda ruwan sama.

Filin wasan na Arthur Ashe shi ne filin wasan tennis mafi girma da ya ke daukar 'yan kallo 22,500.

Gasar Australian Open da ta Wimbledon suna da filayen wasan da ake rufe samansu, yayin da ake shirin samar da irin filin a gasar Faransa zuwa 2018.

An dade ana tunanin ko za a iya yi wa filin gasar tennis din ta Amurka rufin kare ruwan ko ba zai yuwu ba saboda girmansa.

Karin bayani