Luis Suarez ya sauya shawara

luis suarez
Image caption Brendan Rogers ya ce ,''za mu karbe shi da hannu biyu idan ya dawo.''

Dan wasan Liverpool Luis Suarez ba zato ba tsammani ya sauya shawarar barin kungiyar inda yanzu ya ce ba zai je ko ina ba.

Dan wasan dan Uruguay ya matsu ya bar Ingila akan bacin ransa da yadda 'yan jaridar Birtania suke sukan lamirinsa amma kuma klub din nasa baya son rabuwa da shi.

Arsenal wadda ta samu damar shiga matakin wasan Gasar Zakarun Turai ta dauki hanakalin Suarez kuma ta yi kokarin sayen sa a kan fam miliyan 42 kudin da bata taba kashewa akan sayen dan wasa ba amma Liverpool ta ki.

Yanzu Suarez mai shekaru 26 tsohon dan wasan Ajax ya lamunta da matsayin kungiyar na kin sayar da shi.

Ya ce magoya bayan kungiyar sun shawo kansa kan ya ci gaba da zama.

Suarez wanad yake da sauran wasanni shida da ba zai buga ba na hukuncin da aka yi masa kan cizon dan wasan Chelsea Branislav Ivanovic shi ne na biyu da ya fi cin kwallaye a Premier a kakar da ta gabata da kwalaye 23.

A ranar Juma'a ake saran zai koma atisaye da Liverpool bayan wasan sada zumuntar da ya buga wa kasarsa da Japan Larabar nan

wanda suka yi nasar da ci 4-2, ya ci kwalo daya daga ciki.

Karin bayani