Wilshere zai iya zama kyaftin - Gerrard

Jack Wilshere sanye da jar riga
Image caption Wilshere ya kuma samun wani raunin a idon sawunsa, a karshen kakar wasannin da ya gabata

Kyaftin din Ingila, Steve Gerrard ya yi amanna cewa, dan wasan tsakiya Jack Wilshere, zai iya buga wasanni 100 kuma ya zamo kyaftin.

Raunin da Wilshere mai shekaru 21 ya samu ya janyo masa tsaiko, inda ya samu buga wasanni bakwai kacal, tun fitowarsa ta farko a fafatawar da ingila ta yi da Hungary a shekarar 2010.

A lokacin da aka tambayi Gerrard, ko Wilshere zai iya maye gurbinsa nan gaba, sai ya ce "Bani da wani shakku game da hakan."

Wilshere ya samu rauni a idon sawunsa, abin da ya sa bai buga wasa kwata-kwata ba, a kakar wasanni ta shekarar 2011 zuwa 2012.