Wasanninmu na farko na da wahala —Moyes

Image caption David Moyes

Kocin Manchester United David Moyes, ya koka game da wasanni farko da kungiyar za ta buga a kakar wasa ta bana.

Daga cikin wasanni biyar da United za ta buga, za ta hadu da Chelsea da Manchester City da kuma Liverpool.

Moyes ya ce "Ina tunanin wannan ne bude wasa mafi wahala ga Manchester United a cikin shekaru ashirin da suka wuce".

Moyes ya maye gurbin Sir Alex Ferguson ne wanda ya shafe shekaru 26 a Old Trafford.

A makon jiya, tsohon kocin Everton din ya lashe kofin Charity Shield bayan doke Wigan da ci biyu da nema.

Abokan hamayyar United wato Manchester City da Chelsea bisa dukkan alamu su duk wasanninsu babu zafi sosai.

Karin bayani