Mo Farah ya lashe tseren mita 5,000

Image caption Mo Farah

Dan Birtaniya, haifaffen kasar Somalia Mo Farah ya kara kafa tarihi a fagen gudun fanfalaki a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da ake yi a Moscow.

Dan shekaru talatin da haihuwa, Farah ya lashe tseren mita 5,000 bayan nasararsa a tseren mita 10,000 a ranar Asabar.

A tarihi, Mo Farah ne dan wasan na biyu a duniya da ya taba lashe wadanda tseren biyu, bayan nasarar da ya yi a Olympics.

Nasarorin Mo Farah: •2013 Zinare a gasar tseren duniya (10,000m & 5,000m) •2012 Zinare a gasar Olympics (10,000m & 5,000m) •2012 Zinare a gasar Turai (5,000m) •2011 Zinare a gasar tseren duniya (5,000m) da tagulla (10,000m) •2011 Zinare a gasar Turai (3,000m) •2010 Zinare a gasar Turai (10,000m & 5,000m) •2009 Zinare a gasar Turai (3,000m) •2006 Tagulla a gasar Turai (5,000m)

Karin bayani