Roberto Soldado zai sami sauki—Boas

Image caption Saldado zai murmure sosai

Kochiyan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Andre Villas Boas, ya ce dan gaban kulob din nan Roberto Soldado zai sami sauki.

Dan gaban dan kasar Spain an saye shi a kan kudi Pam miliyan 26 a bazara ya kuma ci bugun daga kai sai mai tsaron gida kan kulob din Crystal Palace.

Soldado, mai shekaru 28, ya zura kwallaye 24 a wasanni 35 ga kulob din Valencia kakar wasannin bara.

Kochiyan kulob din Tottenham ya gamsu da yadda tawagar 'yan wasan sa suka buga kwallo a wasan su da Palace.

Karin bayani