CAF: Orlando na jagorantar rukunin A

Image caption Kulob din Orlando ya yi rawar gani a gasar zakaru

Kulob din Afrika ta kudu Orlando Pirates ya lallasa Kulob din Masar zamalek da ci hudu da daya a gasar Zakaru ta Nahiyar Afrika.

Nasarar da Pirates ta samu ya bata damar jagorancin rukunin A.

Wannan nasarar ta biyo bayan wata nasarar da ta samu a kan Al Ahly da ci uku ba ko daya.

Ahly dai ta zama ta biyu a rukunin bayan da ta samu nasara kan AC Leopards ta Congo-Brazzaville.

Zamalek kuwa na matakin karshe a rukunin.

Karin bayani