Arsenal ta taya Yohan Cabaye

yohan cabaye
Image caption Cabaye na shirin buga wasan Newcastle da Manchester City ranar Litinin

Arsenal ta taya dan wasan Newcastle na tsakiya Yohan Cabaye akan kusan fam miliyan goma.

Ko da ike dai Newcastle din kawo yanzu ba ta yi watsi da tayin dan wasan mai shekaru 27 da ke yi wa Faransa wasa ba amma ana ganin tana shirin yin hakan.

Arsenal wadda ta sha kashi a wasanta na farko na Premier da Aston Villa da ci 3-1 a gida ta ki ta yi bayani akan neman dan wasan.

Amma alamu sun nuna cewa kungiyar na neman kara karifnta ne a tsakiya da dan wasan wanda ya yi wa Newcastle wasanni 73 ya ci kwallaye11.

Arsenal din ta gamu da matsalar raunin 'yan wasa da suka hada da Mikel Arteta da Abou Diaby.

Sakamakon rashin nasarar da Arsenal ta yi a wasan nata na farko kungiyar magoya bayan klub din ta soki tsarin sayen 'yan wasanta da kuma kociyan Arsene Wenger.

A ranar Laraba Arsenal za ta yi wasanta na farko na Zakarun Turai da Fenerbahce a Turkiyya.

Karin bayani