FIFA ta amince a buga wasa a Calabar

Image caption Najeriya ce ta lashe gasar kwallon Afrika a 2013

Hukumar kwallon kafa ta duniya-FIFA ta amince a buga wasa tsakanin Najeriya da Malawi a filin kwallon kafa na U.J Esuene dake birnin Calabar.

Wasan na share fage don neman cancantar buga gasar kwallon kafa ta duniya da za ayi a Brazil 2014, ya janyo cece-kuce bayan da Malawi ta bayyana cewar akwai matsalar tsaro a birnin Calabar.

Sai dai rahotanni sun ambato shugaban hukumar kwallon Malawi, Suzgo Nyirenda na cewar sun samu wasika daga hukumar FIFA a kan cewar babu matsala game da tsaro a filin wasan.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya-NFF ta aike wa hukumar FIFA wasikar tabbatar da tsaron filin bayan da 'yan Malawi suka nuna fargabarsu game da tsaro.

A cikin filin wasan na Calabar ne aka buga wasa tsakanin Najeriya da Kenya a watan Maris.

Karin bayani