Fenerbahce na cikin rashin tabbas

Fenerbahce
Image caption Kungiyoyin Besiktas da Kharkiv su ma za su san sakamakon daukaka kararrakinsu

Kungiyar Fenerbahce ta Turkiyya ba za ta san matsayinta ba na karar da ta daukaka kan hanata wasannin Turai sai bayan wasanta da Arsenal na biyu.

A ranar Larabar nan 21 ga watan Agusta Arsenal za ta kara da kungiyar a wasan neman zuwa matakin rukuni na Kofin Zakarun Turai zagayen farko.

A watan Yuni aka haramta wa Fenerbahcen shiga wasannin Turai tsawon shekaru biyu saboda laifin magudin sakamakon wasa.

Amma aka dawo da ita bayan da ta daukaka kara wadda ba a bayyana hukuncinta ba kawo yanzu.

Kotun saurarren kararrakin wasanni ta ce ranar Laraba 28 ga watan Agusta za ta sanar da hukuncin kwana daya bayan karo na biyu na wasanta a gidan Arsenal.

Uefa ta ce ba ta sanar da hukuncinta ba akan matsayin Fenerbahce idan ta ci Arsenal kuma ba ta yi nasara a daukaka karar ba.

Karin bayani