Brazil 2014 : An soma sayar da tikiti

Image caption Tsohon Shugaban hukumar kwallon Brazil, Teixeira da Ronaldo de Lima

An soma sayar da tikitin shiga filayen wasa don kallon gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da za a yi a Brazil a shekara mai zuwa.

Masu sha'awa za su ziyarci shafin Intanet na hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA don su saya tikitin.

Tikiti fiye da miliyon uku ne ake saran za a sayar a lokacin gasar da za a soma daga ranar goma sha biyu ga watan Yunin badi.

Farashin tikitin ya soma ne daga dala 15 na Amurka zuwa dala 1,000 don kallon wasan karshe.

A watan Disamba ne, za a rarraba kasashen da za su fafata zuwa rukuni-rukuni, a don haka duk wanda ya sayi tikiti a yanzu, ba zai san wasan da zai kalla ba.

Karin bayani