Alan Pardew ya zargi Arsenal

alan pardew kociyan newcastle
Image caption Pardew ya damu kan yadda kasuwar musayar 'yan wasa ke ci gaba har bayan fara Premier

Kociyan Newcastle Alan Pardew ya ce bukatar da Arsenal ta gabatar ta sayen Yohan Cabaye ta taimaka wajen lallasa su da Manchester City ta yi da ci 4-0.

Arsenal ta taya dan wasan fam miliyan goma ranar Lahadi, akan haka kociyan ya ki sa Cabaye dan Faransa a wasan nasu na farko na Premier ranar Litinin.

Pardew ya ce, ''ka shirya amfani da gwanin dan wasa kamar wannan sai kawai aka raba ka da shi.''

''Lalle hakan ya shafi wasan namu matuka.''

Ya kara da cewa, ''mai ya sa Arsenal ba za ta nuna sanin yakamata ba ta bari har sai ranar Talata da yamma ta gabatar da tayin dan wasan abin ya daure min kai.''

Arsenal ta nemi Cabaye ne sakamakon sukan da ake wa kungiyar kan rashin sayen 'yan wasa bayan cin da Aston Villa ta yi mata a gida 3-1 ranar Asabar.

Karin bayani