An kori mai horar da 'yan wasan Ingila

hope powell
Image caption Ingila ta ce za ta tuntumi wasu daga ciki da wajen kasar kafin ta nada wadda za ta maye gurbin Powell

An kori mai horar da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta mata ta Ingila Hope Powell.

Mai shekaru 46 Powell wacce ke aikin tun 1998, ta fuskanci suka bayan fitar da Ingila a matakin rukuni na wasan Kofin Turai na 2013 a watan da ya wuce.

Ingila ta yi rashin nasara a wasanni biyu ta yi canjaras, a daya a Sweden kuma wannan shi ne mafi munin zuwansu gasar kasashen Turai tun 2001.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ana ganin tana kokarin maye gurbinta da wata kociyar domin wasan neman zuwa gasar Kofin Duniya da Belarus ranar 21 ga watan Satumba.

Amma kafin sannan ana ganin mai horar da 'yan wasan kasar mata 'yan kasa da shekaru 19 Mo Marley za ta rike aiki.

Sai dai a martanin da ta mayar Powell ta ce akwai bukatar a bunkasa kungiyoyin gida idan ana son kasar ta iya gogayya da takwarorinta da suka ci gaba.

Karin bayani