Chamberlain zai yi jinyar makwanni 6

Image caption Alex Oxlade-Chamberlain

Dan kwallon Arsenal Alex Oxlade-Chamberlain ya bayyana cewar zai yi jinya har zuwa watan Nuwamba saboda rauni a idon sawunsa.

Dan wasan Ingila mai shekaru 20 da haihuwa, ya samu rauni ne a wasan da Arsenal ta sha kashi a wajen Aston Villa da ci uku da daya.

Kocin Gunners, Arsene Wenger ya ce dan wasa zai yi jinyar akalla makwanni shida.

Abinda haka ke nufi shine watakila, Oxlade-Chamberlain ba zai buga wasan Ingila da Moldova da kuma Ukraine a wata mai zuwa don neman cancantar buga gasar cin kofin duniya.

Kawo yanzu Arsenal na fuskantar matsalar 'yan wasan dake fama da rauni ciki hadda, Mikel Arteta a yayinda kuma ta sayar da Andrey Arshavin da Denilson da kuma Sebastien Squillaci.

Karin bayani