An gargadi 'yan wasa shiga kungiyoyi

Turkey_football
Image caption Wasu kungiyoyin ba sa iya biyan albashin 'yan wasansu tsawon watanni

Kungiyar Kwararrun 'Yan wasan Kwallon Kafa ta Duniya ta gargadi 'yan wasa daga kasashe akan su guji shiga klub klub din kasashen Turkiyya da Girka da kuma Cyprus.

Kungiyar ta (FIFPro) damu ne akan yadda wasu kungiyoyin kwallon kafar kasashen ba sa kiyaye ka'idojin kwantiragin 'yan wasa.

Shawarar ta shafi kungiyoyi ne musamman wadanda ba sa cikin gasar Turai.

Kungiyar ta ce wasu 'yan wasan sukan bar gidajen da suke haya dole saboda kungiyarsu ba za ta iya ko kuma ta ki biyan kudin hayarsu.

Sanarwar ta ce an fi samun wannan matsala ne tsakanin 'yan wasa da kungiyoyin kwallon kafa na Cyprus.

Kungiyar 'yan wasan ta Duniya ta ce bayan Cyprus kungiyoyin Girka da Turkiyya su ma suna da wannan matsala wadda ke karuwa kowace shekara.

Tace a dukkanin kasashen bayan daukar dan wasa da watanni sai kugiyoyin su shiga matsalar kudi.

Karin bayani