Arsenal na zawarcin Benzema da Di Maria

Image caption Benzema da Di Maria

Arsenal na kokarin kulla yarjejeniya da 'yan wasan Real Madrid su biyu Karim Benzema da kuma Angel Di Maria.

Gunners na shirin bada fan miliyon 40 a kan dan wasan Faransa, Benzema mai shekaru ashirin da biyar bayan kungiyar ta kasa sayen Gonzalo Higuain da kuma Luis Suarez na Liverpool.

Kocin Arsenal Arsene Wenger na son ya sayi dan wasan Argentina Di Maria, kuma yana zawarcin dan wasan baya da kuma mai tsaron gida.

Wenger ya dade yana muradin Benzema, wanda ya koma Real daga Lyon a kan fan miliyon 30 a shekara 2009, a yayinda shi kuma Di Maria ya koma Bernabeu daga Benfica a shekarar data gabata.

Arsenal dan wasa daya tal ta siya a kasuwar musayar 'yan kwallo wato Yaya Sanogo mai shekaru ashirin daga Auxerre.

Karin bayani