Tattaunawa ta yi nisa akan cinikin Bale

gareth bale
Image caption Real Madrid ta bar riga mai lamba 11 da Bale ke sa wa a Tottenham domin jiransa

Tottenham da Real Madrid sun yi nisa a tattaunawar da suke yi ta cinikin Gareth Bale wanda ake saran komarsa Bernabeau.

Ana saran za a kammala yarjejeniyar a cikin 'yan kwanakin da ke tafe kuma ana saran kudinsa zai zarta dala miliyan 132 da Real Madrid ta sayi Cristiano Ronaldo daga Manchester United a 2009.

Bale mai shekara 24 dan Wales ya zaku ya koma Real Madrid din kuma bai yi wasan Lig din Europa da Tottenham ta yi da Dinamo Tbilisi ba saboda ciwon kafa.

Tottenham ta ci wasan 5-0 a gidan 'yan Dinamon kasar Georgia.

Ranar Alhamis Real Madrid ta je Qatar domin wasa da kungiyar Al Sadd ta tsohon dan wasan Real din Raul wanda a tarihi shi ya fi ci mata kwallo.

Karin bayani