Wallian zai koma Chelsea

Dan wasan tsakiya na Anzhi Makhachkala, Willian
Image caption Chelsea za ta sayi dan wasan a kan kudin da Tottenham ta biya, amma ta kara kawata kwantiragin

Manajan kulob din Chelsea, Jose Mourinho ya ce dan wasan kulob din Anzhi Makhachkala, Willian ya amince ya koma kulob din a kan fan miliyon 30.

Dan wasan tsakiyar mai shekaru 25 ya yi gwajin lafiya da Tottenham, amma zai iya sa hannu a kwantiragin Chelsea a ranar Alhamis, bayan kulob din ya shiga zawarcinsa.

Tottenham ta zaci Willian zai zamo babban dan wasa na biyar da za ta saya, amma shugaban Chelsea Roman Abramovich ya yi amfani da sanayyarsa a Anzhi.

Willian ya koma Anzhi ne a watan Janairu a kan kudi fam miliyan 30, bayan ya shafe kakar wasanni biyar da rabi a kulob din Shakhtar Donetsk na Ukrain.