Cardiff ta casa Man City

cardiff ta casa mancity
Image caption Tsohon matashin dan wasan Man United Campbell ya daga ragar Man City sau biyu cikin minti takwas

Cardiff City ta casa Manchester City da ci 3-2 a wasan Premier.

Dzeko ne ya fara ci wa Man Ciy bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 52.

Minti takwas tsakani sai Gunnarsson ya rama wa masu masaukin baki.

A minti na 79 sai Campbell ya kara ta biyu sannan kuma ya sake ci a minti na 87.

Wannan ita ce nasarar Cardiff ta farko a gasar ta Premier a wasansu na biyu da hakan

ya sa ta zama ta 11 a tebur da maki uku da bashin kwallo daya.

Manchester City kuma ta fado zuwa ta shida da maki 3 da kwallaye 3 a wasanni biyu.