Karon Man United da Chelsea

chelsea da man united
Image caption A haduwarsu 42 ta Premier Chelsea ta yi nasara sau 14 United sau 13, canjaras kuma 18.

Manchester United za ta karbi bakuncin Chelsea a wasanta na farko na gida ranar Litinin.

Dole ne kociyan Man United David Moyes ya yanke shawara akan sanya Rooney.

A wasan da kungiyar ke neman Rooney haikan.

Chelsea ta taya shi sau biyu kuma Mourinho ya ce za su sake tayi na uku amma sai bayan karawar tasu.

'yan wasan United da ba za su buga ba saboda rauni su ne Rafeal da nani da Ashley Young da kila Javier Hernandez.

David Luiz ma watakila ba zai buga wasan ba saboda rauni a cinya da yake fama da shi.

David Moyes ya nuna damuwarsa kan hada kungiyarsa da manyan kungiyoyi a farkon gasar.

Shekaru tara shi ma Mourinho ya yi wannan korafi a farkon kama aikinsa a Chelsea.

Sai dai Chelsean ta yi nasara a wancan lokacin a gida.

A Premier da ta wuce Chelsea ta yi nasara a Old Trafford 1-0.

Manchester United kuma ta yi galaba a Stamford Bridge 3-2.