Wenger: na musamman kawai zan saya

arsene wenger
Image caption Arsene Wenger ya ce ba zai bayyana sunayen 'yan wasan da yake nema ba

Arsene Wenger ya ce 'yan wasa na musamman kawai zai saya yayin da ya rage sati daya a rufe kasuwar sayen 'yan wasa.

Yaya Sonogo ne dan wasan da Gunners din suka saya kawai kawo yanzu.

Amma kungiyar na son sayen Karim Benzema da Angel Di Maria na Real Madrid da Yohan Cabaye na Newcastle.

Wenger wanda ya yi nuni da 'yan wasansa da suka ci Fulham 3-1 ya ce 'yan wasa ne na musamman.

Saboda haka idan zai karo wani dan wasan to shi ma zai zama na musamman ne.

Ana ganin Mathieu Flamini wanda yake atisaye da kungiyar a bazaran nan yana tattaunawa akan dawowarsa bayan ya bar klub din ya tafi AC Milan a 2008.

Ana kuma ganin kungiyar za ta sayo mai tsaron gida da dan wasan baya kafin karshen wa'adin kasuwar ranar 2 ga Satumba.