Wata kungiya na neman Gareth Bale

gareth bale
Image caption Tottenham na duba bukatar daya kungiyar da ta ke son sayen Gareth Bale

Wata kungiya ta mika bukatarta ta sayen Gareth Bale bayan Real Madrid da ta taya shi akan fam miliyan 86.

Hukumomin klub din na Tottenham da suka sanar da haka sun ce har yanzu basu cimma yarjejeniya da Real Madrid ba.

Ba a bayyana kungiya ta biyu da ta nuna bukatar sayen dan wasan ba amma dai Manchester United an san tana sonsa.

Tottenham ta nemi Chelsea ta sayar mata wani dan wasa domin maye gurbin Bale

Kociyan Tottenham Andre Villas-Boas ya ce suna tsammanin Bale ya dawo daga Madrid ranar Talatar nan idan ba a cimma yarjejeniya ba.