Kociyan Malawi zai kai keshi kara

tom saintfiet
Image caption Saintfiet ya ce, ''neman da muka yi a sauya wurin wasan ba wani muka ci wa mutunci ba''

Kociyan Malawi Tom Saintfiet ya ce zai kai takwaransa na Najeriya Stephen Keshi kara gaban Fifa akan wariyar launi.

Saintfiet ya zargi Keshi da ce masa, ''farar fata wanda ya kamata ya koma Belgium.

Saintfiet ya ce, ba abu ne da za a lamunta ba a ce wani ya furta wadannan kalamai, bambamcin launin fata ne karara.''

Kociyan na Malawi wanda ya auri 'yar Zimbabwe a farkon watannan ya shedawa BBC cewa kalaman na Keshi sun girgiza shi.

Kuma yana ganin za su iya haddasa rikici a lokacin wasan na ranar 7 ga watan Satumba.

Kociyoyin na sa-in-sa ne tun lokacin da Malawi ta bukaci Fifa ta sauya Calabar a matsayin wurin wasansu na neman zuwa gasar Kofin Duniya na wata mai zuwa saboda tsaro.

Duk kasar da ta yi nasara a karawar ita za ta wakilici rukuninsu da za ta hadu da sauran kasashe tara.

Daga cikin goman ne kuma za a fitar da biyar da za su wakilici Afrika a gasar Kofin Duniya.

Karin bayani