Bale ya ki halattar atisayen Tottenham

gareth bale
Image caption Bale bai halarci wasan Tottenham da Swansea ba amma kociyansu ya kare shi

Gareth Bale ya ki halattar atisayen Tottenham kamar yadda kungiyar ta bukace shi da yi bayan hutun da ta ba shi.

Kungiyar ta bukaci dan wasan mai shekara 24 ya dawo ya ci gaba da atisaye da takwarorinsa ranar Talatar nan amma kuma ba a sanar da dalilin rashin bayyanar tasa ba.

Kociyan kungiyar Andre Villas-Boas ya ce sun ba wa Bale hutun kwana biyu.

Bale wanda Real Madrid ta taya fam miliyan 86 Tottenham ta ce ba ta cimma yarjejeniya da ita ba.

Tottenham din ta kuma sami wata bukatar ta sayen dan wasan bayan ta Real din sai dai ba a sanar da kungiyar da ta gabatar da bukatar tasa ba.

Amma dai ana danganta Manchester United da bukatar sayen dan wasan a wannan lokacin na musayar 'yan wasa.

Sai dai kuma rahotanni sun ce tuni aka kafa wani dandamali mai lakabin ''dandamalin Bale'' a filin wasan Real Madrid wanda za a bayyana shi ga magoya bayan kungiyar.

Karin bayani