Ingila ta gayyaci Townsend da Barkley

Townsend da Barkley
Image caption Townsend da Barkley 'yan wasan tsakiya ne

Kociyan Ingila ya gayyaci dan wasan Everton Ross Barkley dan shekara 19 da na Tottenham Andros Townsend mai shekara 22 a tawagar kasar.

Kociyan ya gayyaci 'yan wasan biyu da ba su taba yi wa Ingila wasa ba domin wasan neman zuwa gasar Duniya.

Ingilan za ta yi wasan neman cancantar zuwa gasar Kofin Duniya da Moldova da kuma Ukraine.

Roy Hodgson wanda ya ce, ''muna son mu yi nasar ne shi yasa kuma 'yan wasan biyu za su iya bada mamaki.''

Ranar 6 ga Satumba Ingila za ta kara da Moldova a Wembley kafin 10 ga watan Satumban ta je wa Ukraine.