Tottenham za ta ci tarar Gareth Bale

Image caption Gareth Bale

Watakila Tottenham taci tarar dan wasanta Gareth Bale wanda Real Madrid ke zawarcinsa, saboda kin zuwa horo a kwanaki biyu a jere, kamar yadda kocinsa Andre Villas-Boas ya bayyana.

Real Madrid ta shirin maida shi dan kwallon mafi tsada a duniya a kan fan miliyon 86.

An shirya Bale mai shekaru 24 zai koma horo a ranar Talata bayan hutun da aka bashi.

Villas-Boas yace " ana batun cefanar dashi zuwa Real Madrid, idan har aka daidaita muna masa fatan alheri, amma ba daidai bane mutum yaki zuwa horo".

Tottenham na jan kafa wajen cefanar dashi har sai ta samu wanda zai maye gurbinsa.

Spurs na zawarcin dan kwallon Argentina wanda ke taka leda a Roma Erik Lamela, bayan dan Brazil da take muradi ya koma Chelsea.

Karin bayani