Abdul Ajagun ya koma Panathiniakos

Image caption Abdul Jaleel Ajagun

Dan kwallon Najeriya Abdul Jeleel Ajagun ya koma kungiyar kwallon kafa ta Panathinaikos a kasar Girka daga kungiyarsa Dolphins FC.

Dan wasan mai shekaru 20 ya sanya hannu a yarjejeniyar shekaru hudu don taka leda a kulob din.

Ya jagoranci Najeriya ta kasance ta uku a gasar kwallon matasan duniya 'yan kasada shekau 20.

Ajagun ya buga kwallo a Dolphins na tsawon shekaru biyar daga shekara ta 2008 zuwa 2013 inda ya zira kwallaye 39 a cikin wasanni 92.