Tottenham ta sayi Eriksen daga Ajax

Image caption Christain Eriksen

Tottenham ta sayi dan kwallon Ajax, Christian Eriksen a kan fan miliyon goma sha daya da rabi.

Dan kwallon Denmark mai shekaru 21, ya buga wa Ajax wasanni 161 inda ya zira kwallaye 32.

Shi ne dan kwallo na uku da Spurs ta siya bayan ta sayi dan kasar Romania Vlad Chiriches da kuma dan Argentina Erik Lamela.

Daga sayen Eriksen, kenan Tottenham ta kashe kusan fan miliyon 105 a kasuwar musayar 'yan kwallo ta bana a yayinda ta ke shirin sayarwa da Real Madrid Gareth Bale a matsayin dan kwallon da yafi kowanne tsada a duniya.