Arsenal ta ci abokan hamayya Tottenham

giroud ya ci wa arsenal tottenham
Image caption Wannan ce kwallo ta hudu da Giroud ya ci a kakar nan

Arsenal ta ci gaba da tarihin nasara a gidanta akan abokan hamayyarta na arewacin London Tottenham da ci 1- 0.

Olivier Giroud ne ya ci Tottenham a wasan da ta yi rashin nasararta ta farko a wannan kakar a minti na 23 da fara wasa.

Yanzu Arsenal ta zama ta hudu a tebur a wasanni uku da maki shida da kuma kwallo daya.

Tottenham ita ma tana da maki shida da kwallo daya a wasanni uku amma ita ce ta shida a bayan Stoke ta biyar.

Sau daya kawai Tottenham ta ci Arsenal a gidan Gunners tun 1993.

A shekaru biyu da suka gabata Arsenal ta ci Tottenham 5-2 sau biyu a gida.

West Bron da Swansea

Swansea kuwa ta bi West Brom har gida ne ta yi mata 2-0 inda Ben Davies ya fara ci a minti na 22

sannnan kuma can a minti na 83 Pablo Hernandez ya kara ta biyu.

Swansea ce ta 16 a tebur da wasa uku, bashin kwallo uku da maki uku ita kuma West Brom ta karshe

(20) da bashin kwallo a wasanni uku da kuma maki daya.

Karin bayani