Bale ya koma Real Madrid

gareth bale
Image caption ''na yi shekaru shida na farin ciki a Tottenham amma yanzu lokacin tafiyata ya yi'' inji Bale

Real Madrid ta kafa sabon tarihi a fagen cinikin 'yan wasan kwallon kafa da ta sayi Gareth Bale akan fam miliyan 85.

Dan wasan na Tottenham dan Wales ya amince a rika biyan sa fam miliyan 300 000 a sati tsawon shekaru shida a klub din.

Cinikin nasa na fam miliyan 85.3 (euro miliyan100) ya sha gaban na Cristiano Ronaldo da Real ta saya fam miliyan 80 a 2009.

Za a tantance lafiyar dan wasan mai shekaru 24 kafin a gabatar da shi a filin wasan kungiyar ranar Litinin da karfe 12: na rana agogon Najeriya.

Karin bayani