Real Madrid ta gabatar da Bale

Image caption Gareth Bale

An gabatar da Gareth Bale ga magoya bayan Real Madrid inda ya kafa sabon tarihi a fagen cinikin 'yan wasan kwallon kafa.

Dan kwallon na kasar Wales ya samu gagarumar tarba a filin Bernabeu inda magoya baya 20,000 suka halarta domin kalonshi.

Bale ya daga rigar kwallo mai lamba 11 sannan ya dan murza leda a cikin filin.

Tsohon dan wasan na Tottenham ya amince a rinka biyan sa fam miliyan 300 000 a duk mako na tsawon shekaru shida a kulob din.

Bale ya shiga sawun manyan 'yan kwallo da suka buga wa Real wato "Galacticos" irinsu Zinedine Zidane,Ronaldo da David Beckham da Figo da Roberto Carlos.

Karin bayani