Kaka ya koma AC Milan daga Real

Image caption Angulu ta koma gidanta na tsamiya

Dan kwallon Brazil Kaka ya bar Real Madrid inda ya kara komawa tsohon kulob dinsa AC Milan.

Dan wasan mai shekaru 31, Real ta sayi shi a kan fan miliyon 56 a watan Yunin 2009.

Tsohon gwarzon dan kwallon duniya a shekara ta 2007, Kaka ya kulla yarjejeniyar shekaru biyu tare da Milan.

A shekara ta 2003 ya bar Sao Paolo a matsayin matashi, sannan ya koma AC Milan inda ya lashe gasar zakarun Turai da ta Serie A a shekaru shida daya shafe a Italiya.

A Real Madrid kuwa ya daga kofin La Liga dana Copa del Rey da kuma Spanish Supercup.

Kaka ya zira kwallaye 29 a wasanni 87 da ya bugawa Brazil sannan ya buga gasar cin kofin duniya sau uku.

Karin bayani