Ozil ya koma Arsenal daga Real

Image caption Mesut Ozil

Arsenal ta kulla yarjejeniyar Euro miliyon 50 da Real Madrid a kan sayen dan kwallon Jamus, Mesut Ozil.

Dan kwallon mai shekaru 24 ya amince ya koma kungiyar amma za a gwada lafiyarsa a Arsenal kafin su kamalla kulla yarjejeniyar.

A yanzu haka Ozil yana Jamus kuma a can za a gwada lafiyarsa.

Arsenal ta gamu da cikas a kokarin sayen dan wasan Lievrpool Lius Suarez da dan Real Gonzalo Higuain.

Real Madrid ta saki Ozil ne bayan da Gareth Bale ya koma Bernabeu daga Tottenham.

Ozil ya koma Real daga Werder Bremen shekaru uku da suka wuce a kan fiye da fan miliyon 12.