Reading na tattaunawa da Sissoko

mohamed sissoko
Image caption Ana saran Reading za ta dauki Mohamed Sissoko

Reading tana tattaunawa da tsohon dan wasan tsakiya na Liverpool Mohamed Sissoko.

Bayan da aka kawo karshen kwantiraginsa da Paris St-Germain ranar Litinin.

Dan wasan na Mali mai shekara 28 ya shafe sheakaru biyu da rabi a Liverpool kafin ya tafi Juventus a shekara ta 2008.

Daga can ne kuma ya koma Paris St-Germain bayan shekaru uku.

Kungiyar Reading za ta iya daukarsa saboda duk da cewa an rufe kasuwar sayen 'yan wasa ta bazaran nan.

Saboda babu wani kwantiragi a kansa na wata kungiyar kwallon kafa.