Nigeria da Malawi: 'Yan wasa 17 sun iso

Image caption 'Yan wasan Super Eagles

'Yan wasan Super Eagles su 17 sun isa birnin Calabar a shirye-shiryen Najeriya na fuskantar kasar Malawi a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin kwallon duniya da za a yi a karshen mako.

Rahotanni sun nuna cewar kawo yanzu manyan 'yan wasa kamarsu Vincent Enyeama da John Mikel Obi da Victor Moses da kuma Ahmed Musa suna jihar ta Cross Rivers don wasan.

Tun a ranar Talata 'yan wasan suka soma horo don shiryawa fafatawar.

Najeriya na bukatar nasara ko kuma a tashi canjaras da Malawi don ta samu damar kaiwa bugun kifa daya kwala, kafin tsallakewa zuwa gasar da za a buga a Brazil a shekara ta 2014.

Karin bayani