'Ingila ba za ta iya lashe gasar 2014 ba'

Image caption Tawagar 'yan kwallon Ingila

Shugaban hukumar dake kula da kwallon kafa a Ingila, Greg Dyke ya ce bai saran Ingila ta lashe gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil a shekara mai zuwa.

Dyke ya shaidawa taron manema labarai a ranar Laraba a London cewar yanason tawagar 'yan kwallon Ingila ta kai zagayen kusada karshe a gasar cin kofin kwallon kasashen Turai a shekara ta 2020 sannan ta lashe kofin duniya a 2022.

A hirarsa da BBC, ya ce "hakan ba yana nufin Ingila ba za ta taka rawar gani ba a Brazil a shekara ta 2014".

Ingila za ta buga wasanni biyu don kokarin samun gurbin zuwa gasar cin kofin duniya a badi.

Tawagar Roy Hodgon a ranar Juma'a za ta kara da Moldova a filin Wembley sannan kuma ta hadu da Ukraine a Kiev a ranar Talata mai zuwa.

A yanzu haka dai Ingila ce ta biyu a rukunin H, inda Montenegro ke gabanta da maki biyu.

Karin bayani