Wawrinka ya yi waje da Murray

stanislas wawrinka
Image caption ''Ina ganin watakila yau ba ranata ba cei'' in ji Andy Murray

Andy Murray ya kasa kare kofinsa na gasar tennis ta Amurka a karawarsa da Stanislas Wawrinka.

Wawrinka ya yi wa je da shi a wasan gab da na kusa da karshe na gasar da maki 6-4 6-3 6-2.

Stanislas Wawrinka na tara a duniya dan Switzerland ya yi galaba a kan Murray na uku a duniya.

Wannan na daya daga manyan nasarorin da Wawrinka ya taba yi da ta sa Murray zai rasa kofinsa a ranar Litinin.

Karin bayani