Nani ya sabunta kwantiragi

luis nani
Image caption Moyes ya ce ya ji dadi Luis Nani ya sabunta kwantiraginsa

Dan wasan Manchester United Luis Nani ya sabunta kwantiraginsa da kungiyar na karin shekaru biyar.

Nani dan kasar Portugal yanzu zai ci gaba da zama a Manchester United har zuwa watan Yuni na 2018.

Dan wasan mai shekaru 26 ya ci kwallaye 40 a wasanni 217 tun da ya koma Manchester United daga Sporting Lisbon a 2007.

A zamansa a Man U na shekara shida Nani ya dauki kofuna takwas da suka hada da Premier hudu da kuma na Zakarun Turai.

Kafin yanzu ana shakkun ci gaba da zamansa a kungiyar ganin cewa wasanni bakwai kawai ya buga a kakar wasannin da ta wuce.

Karin bayani