Arsenal za ta dauki kofi in ji Ozil

mesut ozil
Image caption Ozil ya ce, ''Ina son in inganta wasana a karkashin Wenger''

Dan wasa mafi tsada da Arsenal ta saya Mesut Ozil ya ce yana da kwarin guiwa kungiyar za ta kawo karshen shekaru takwas na rashin daukar kofi a bana.

Ozil mai shekara 24 ya kulla yarjejeniyar shekaru biyar da kungiyar daga Real Madrid a kan fam miliyan 42.2 a ranar karshe ta sayen 'yan wasa.

Dan wasan na Jamus ya ce klub din zai iya sake daukar kofi a karon farko a bana tun bayan na FA da ya dauka a 2005.

Ya ce, ''Arsenal ba ta dace da nasara ba a 'yan shekarun da suka gabata amma kuma yanzu muna son mu kara zama masu nasara.''

Ozil ya ce sha'awarsa da Arsene Wenger da kuma yadda kociyan yake taimaka wa 'yan wasa su farfado suka sa ya yarda ya dawo Arsenal.