Rooney ya kare kansa da hoton rauni

wayne rooney ya ji rauni
Image caption Rooney na daya daga cikin 'yan wasan Ingila uku da suka ji rauni

Wayne Rooney ya sanya hoton kansa da raunin da ya ji a shafin intanet na Facebook domin kare kansa daga zargi.

Phil Jones ne ya ji wa Rooneyn rauni a kansa da kafa bisa kuskure lokacin da suke atisaye a kungiyarsu ta Man U.

Hadarin ya faru ne ranar Asabar kafin wasansu da Liverpool wanda Rooney bai yi ba saboda raunin.

Wasu na tantama ne a kan ficewa da ya yi daga tawagar da za ta yi wa Ingila wasan neman shiga gasar Kofin Duniya.

''Ya ce wasu na shakkun kishin kasata saboda na janye daga wasannin biyu na ranar Juma'a da Talata.''

''Na tabbata yanzu mutane za su ga dalilin da ya sa ba zan yi wasannin ba.''

Kociyan Manchester United David Moyes ya ce dan wasan watakila zai yi jiyya tsawon makwanni uku.

Ranar Juma'a Ingila za ta kara da Moldova sannan ta tafi Ukraine ranar Talata a wasannin neman zuwa gasar ta Duniya da za a yi a 2014.