Ribar Real Madrid ta karu da kashi 50

Image caption Sabon dan kwallon Real Madrid, Gareth Bale

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bayyana samun kimanin euro miliyan 520 a kakar wasa ta 2012 zuwa 2013, matakin da ta cimma shekaru biyu a jere.

Hakan na nufin ta samu kari a kan kudin da ta samu a kakar wasannin ta na bara da kaso daya da digo uku bisa dari.

Da haka kungiyar ta Real Madrid ta zama kungiyar wasanni daya tilo a duniya da kudin shigarta ya haura euro miliyan 500.

Ta kuma samu ribar kimanin euro miliyan 36, wato kashi hamsin da biyu cikin dari, idan aka kimanta da shekarar bara.

Hakazalika bashin da ake bin kungiyar ya ragu da kimanin kashi 27 cikin dari zuwa euro miliyon 90, wato ragin kwatankwacin euro miliyon 34.

Wannan diddigar dai yi la'akari ne da manufofin kungiyar na saye/sayar da 'yan wasa bara.

Lissafin bai yi la'akari da sayen Gareth Bale, da Isco, da Asier Illarremendi, da Dani Carvajal da da Casemiro ba, wadanda jimillar kudinsu ta kai kimanin euro miliyan 181 da kuma sayar da Mesut Ozil, Gonzalo Higuain, Jose Callejon da Raul Albiol.

Karin bayani