Matsayin Bale a Real Madrid

Gareth Bale
Image caption Gareth Bale yana da kokarin shiryawa abokanan wasa kwallo su ci

Sabon dan wasan Real Madrid Gareth Bale zai koma matakin mai jefa kwallo a raga(striker).

Paul Clement mataimakin mai horar da Real Madrid ya ce, Madrid ta dade tana duba inda dan wasan ya kamata ya buga domin fito da hazakarsa.

Gareth yana da kwarewa da hazakar jefa kwallo a raga, ya kuma kware da wasan tsakiya.

Carlo Ancelotti ya ce zai yi amfani da kwararrun yan wasan da kungiyar take dasu domin samun sakamako mai kyau.

Karin bayani