Kungiyar kwallon Kamaru ta kai gacci

Cameroon World Cup
Image caption Kamaru ta kai matakin karshe na samun shiga gasar cin Kofin Duniya.

Kamaru ta kai ga ci a wasan kofin Duniya, bayan da ta samu nasara a kan Libya da ci 1-0, a wasan da suka kara ranar Lahadi a Yaounde.

Sauran kasashen da za su fafata don fitar da wadanda zasu wakilci Africa su ne.

Algeria da Burkina Faso da Cape Verde da Masar da Ethiopia da Ghana da Ivory Coast da Najeriya da Senegal.

Za a fitar da jadawalin wasanninsu ranar 16 ga watan Satumba a Alkahira, sannan za su kara a cikin watan Oktoba da Nuwamba.