An dawo da wasan kokawa a Olympics

kokawar turawa
Image caption An shire kokawar turawa a Olympics sakamakon rashin zamanantar da wasan.

Kwamitin wasan Olympics ya kada kuri'ar amincewa da dawo da wasan kokawar turawa cikin gasar.

Yanzu za'ayi wasan a gasar shekarar 2020 da birnin Tokyo zai karbi bakunci.

Tun a farkon shekarar nan kwamitin ya fitar da wasan kokawar sakamakon rashin zamanantar da shi.

Kokawar turawan ta yi galaba ne a kan wasannin squash da kwallon baseball da kuma softball.

A watan Fabrairu aka fitar da wasan na kokawar turawa daga jerin wasannin da ake yi a gasar.